Kano Ayau Hausa, Siyasa

Za a bude mana ofishinmu na Borno-Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah-wadai da rufe hedikwatar jam’iyyar da gwamnatin Jihar Borno ta yi.

BBC ta kalato daga cikin wata sanarwa da Kwankwason ya fitar a shafinsa a Twitter, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankali da kuma bin doka da oda

Ya kara da cewa suna yin duk abin da ya kamata wajen ganin an bude sakatariyar jam’iyyar da aka garkame.

Lamarin na faruwa ne yayin da Kwankwason ke shirin zuwa jihar a ƙarshen wannan makon.

Leave a Reply