Labarai

Yariman Saudiyya na da matsalar kwakwalwa- Sanatocin Amurka

Sanatocin Amurka sun ce yanzu sun hakikance cewa yariman Saudiyya na da hannu cikin kisar Jamal Khashoggi bayan da hukumar leken asirin kasar ta gabatar masu da wani bayani.

A wata caccaka da ya yi, sanata Lindsey Graham ya ce ya tabbatar Mohammed bin Salman na da hannu a kisan dan jarida Jamal Khashoggi.

Sanatan na jam’iyyar Republican daga yankin South Carolina ya bayyana yariman na Saudiyya a matsayin mutum ‘mai ta’adi’, ‘mahaukaci’, kuma ‘mai hadari’.

Saudiyya dai ta gurfanar da mutum 11 gaban kotu, amma ta musanta cewa yariman na Saudiyya na da hannu cikin al’amarin.

Me sanatocin suka ce?

Daya daga cikin sanatocin na Amurka ya ce ba zai kara goyon bayan kasar Saudiyya a yakin da take yi a Yemen ba, ko kuma sayar wa kasar da makamai, matukar yariman na kan mukaminsa.

Wani sanatan kuma mai suna Bob Corker ya shaida wa ‘yan jarida cewa a yanzu ba ya tantama ko kadan, cewa Mohammed bin Salman ne ya bayar da umurnin aiwatar da kisan.

Mista Corker ya ce shugaban Amurka Donald Trump ya nuna goyon baya ke nan ga kisan dan jaridan saboda ya ki sukar yariman na Saudiyya.

Majalisar dai tana shirin kada kuri’a kan wata shawara ta daina tallafa wa kawancen dakaru karkashin Saudiyya wadanda ke fada da ‘yan tawaye a Yemen kamar yadda BBC ta ruwaito.

Leave a Reply