GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Yarima Charles ne zai zama sabon Sarkin Ingila

Babban danta Charles, tsohon Yarima na Wales, ne zai jagoranci kasar wajen jimami a matsayinsa na sabon Sarki da kuma shugaban kasashe 14 na kungiyar Commonwealth.

A sanarwar da Fadar Buckingham ta fitar ta ce: “Sarauniya ta rasu salin-alin a Balmoral da rana.

“Sarki da mai dakinsa za su ci gaba da kasancewa a Balmoral da wannan maraice kuma za su koma London gobe,” kamar yadda BBC ta ruwaito.

Dukkan ‘ya’yan Sarauniya sun tafi Balmoral, kusa da Aberdeen, bayan likitoci sun sanya ido sosai kan Sarauniya.

Jikanta, Yarima William, shi ma yana can, tare da dan uwansa, Yarima Harry, yana kan hanyar zuwa Balmoral.

Leave a Reply