Kano Ayau Hausa, Labarai

‘Yan ta’addan sun haramta harkokin siyasa a wasu yankunan Kaduna

Kungiyar ‘Yan ta’addan Ansaru dake kai hare hare a Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ta mamaye wasu Yankunan Gabashin karamar hukumar Birnin Gwari dake Jihar Kaduna, inda ta haramta gudanar da harkokin siyasa.

Shugaban kungiyar Ci gaban Masarautar Birnin Gwari Ishaq Kasai ya bayyana haka ga Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriyar, inda yace yanzu haka kungiyar na daukar matasa a yankin da kuma aurar da ‘yan mata.

Mamaye Mazabu 7

Kasai yace kungiyar na da sansanoni a mazabu guda 7 dake Gabashin karamar hukumar, inda suke lakadawa wadanda suka gani da hotunan ‘yan takarar siyasa daga kowacce Jam’iyya duka a yankunan da suke iko da su.

Shugaban kungiyar Ci gaban yace kungiyar Ansarun na samun karbuwa tsakanin mazauna yankin abinda ke bata damar janyo hankalin matasa musamman a mazabun Tsohuwar Kuyello da Damari dake mazabar Kazage, inda yace ko a cikin wannan mako biyu daga cikin ‘yayan kungiyar na shirin gudanar da aure a bikin da aka shirya yi ranar asabar mai zuwa.

Sharrudan aure

Kasai yace kungiyar ta kuma gindaya sharruddan auran, wanda ya kunshi daukar amaren zuwa cikin daji ba tare da kayan gara ba, sai dai kawai katifa da kwanukan cin abinci kamar yadda ka’idar su take.

Shugaban kungiyar yace yanzu haka hankalin jama’ar yankin a tashe yake saboda ayyukan ‘yayan kungiyar musamman hana harkokin siyasa, ganin yadda lokacin zabe ke zuwa a matakai daban daban.

Ya zuwa yanzu babu wata majiyar hukuma da ta tattabar da ayyukan kungiyar a Birnin Gwari, daga bangaren Yan sanda zuwa ma’aikatar tsaron jihar Kaduna.

Leave a Reply