Hukumar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta musanta labarin cewa an samu rasuwar mutum guda a mazabar Boi da ke Karamar Hukumar Bogoro a Jihar Bauchi.
Biyu daga cikin ’yan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC a Jihar, Farfesa Muhammad Ali Pate da Dokta Ibrahim Yakubu Lame ne suka sanar da batun mutuwar mutumin da ba a bayyana sunansa ba, yayin da suke jawabi ga manema labarai dangane da rashin ingancin zaben fid da gwani na Jam’iyyar APC da aka yi a jihar.
Kakakin ’Yan sandan Jihar, DSP Kamal Datti Abubakar ya ce ’yan sanda ba su da masaniya kan lamarin amma zai bincika. Bayan da ya bincika sai ya sake kiran ’yan jarida ya bayyana cewa babu wani mutum da ya rasu a garin, lokacin zaben fid da gwanin.
Jam’iyyar APC na fama da rikicin cikin gida, wanda wannan dalili ya sa aka zartar da cewa a yi zaben ’yar Tinke a zaben fid da gwanin da nufin yin adalci ga dukan ’yan takara.
Sai dai a ranar da za a yi zaben da dare, ’yan takara uku daga cikin hudu, Dokta Ibrahim Yakubu Lame da Farfesa Muhammad Ali Pate da Kyaftin Muhammad Bala Jibrin sun bayyana cewa dukan ka’idojin da uwar jam’iyyar ta shimfid wajen gudanar da wannan zabe na fid da gwani ba a bi su ba.
Sun ce ba a gudanar da zaben fid da gwanin ba, domin kusan a dukan mazabu ba inda aka kai isassun katunan jefa kuri’a. Sun kuma yi zargin cewa ’yan sanda da sojoji sun yi ta razana masu zabe. An kuma harba barkonon tsohuwa a wasu mazabu, an kuma ji wa wadansu magoya bayansu rauni, mutum guda kuma ya rasu a Boi sannan an bugi wadansu daga cikin magoya bayansu a shiyyar Bauchi ta Arewa.
Sun yi kira ga uwar jam’iyyar ta soke zaben kuma sun sha alwashin kaurace wa dukan zabubbukan da za a yi na fid da gwani a jam’iyyar, har sai ko an kori Gwamna Abubakar daga jam’iyyar kuma an dakatar da shugabancin zartarwa na jam’iyyar a jihar.
Duk da wannan korafi, bai hana jam’ian da suka gudanar da zaben bayyana sakamakon zabubbukan da suka ce an gudanar ba, inda babban jami’in da ke karbar sakamakon zaben, Farfesa Mohammed Ahmed Bakori ya ce an yi zabe kuma ya bayyana Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin wanda ya lashe da kuri’a 75,086 sai Dokta Ibrahim Yakubu Lame ya samu kuri’a 3,988 sai Farfesa Ali Pate ya samu kuri’u 2,886, yayin da Kyaftin Bala Jibrin ya samu kuri’u 2,539.
A wata zantawa da manema labarai, Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar ya ce wadannan korafe-korafe da ’yan siyasa ke yi, gishiri ne a harkokin siyasa amma Allah Yake ba da mulki ga wanda Ya so, a lokacin da Ya so.
Gwamnan ya ce dukan ’yan takarar Jam’iyyar APC, uwar jam’iyyar ta kasa ta yi musu duk abin da suke bukata da nufin yin adalci kuma al’umma sun sake zabensa ne saboda kyawawan ayyukan da gwamnatinsa ke gudanarwa a jihar.
Ya ce zai bi dukan matakai domin sasanta tsakaninsa da dukan ’yan takarar domin samun zama lafiya mai dorewa a Jihar Bauchi. Ya ce tuni ya fara tattaunawa da wadanda suka fadi daga cikin ’yan takarar, domin samun maslaha. Ya gode wa ’ya’yan jam’iyyar da suka fito suka sake zabensa.