Kano Ayau Hausa, Labarai

‘Yan sanda sun kama ‘yan daba da suka addabi Kano

Hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu matasa su kusan 45 da suke yawo ɗauke da makamai da ƙwayoyi.
Da yake bayyana lamarin a yau Litinin, kakakin hukumar, SP Abdullahi Kiyawa ya ce an sami muggan makamai a hannun ‘yan daban tare da tarin ƙwayoyi. Rundunar Operations Puff Adder ce ta yi musu ƙawanya kuma suka sami damar daƙume su.
‘Yan ta’addan sun nufi Filin Mahaha ne inda suke shirin yi wa mutane ta’addanci.
SP Kiyawa da yake zantawa da majiyar TDR Hausa, ya ce hukumar ta sami kira ne ta kan lambobinsu na kar-ta-kwana; 08032419754 da 08123821575, cewa an ga giftawar ‘yan daban, inda nan da nan suka bi su suka cafke su a wuraren Kofar Na’isa da Kwana Disu.
Hukumar ta yi kira ga al’umma da su cigaba da kawo rahoton dukkanin wasu ɓata-gari ko kuma wani motsi da ba a gamsu da shi ba.

Leave a Reply