Labarai

’Yan Sanda Sun Bankado Haramtattun Bindiga 47 A Kano

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta ce, ta kwato haramtattun bindigogi 47, albarusai 819 da mazubin harsasai 1,117, a tsakanin watan Janairu zuwa na Agusta 2018. Hakan yana cikin sanarwar da Kakakin rundunar, Magaji Majiya, ne ya sanya wa hannu, ya kuma rabawa manema labarai ranar Talata a Kano. Majiya ya ce, hakan yana cikin umurnin da shugaban ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, ne ya bayar na tabbatar da raba mutanan da ba su da izini mallakan bindigogi da albarusai. Majiya ya ce, an kwato bindigogi da albarusan ne daga hannun wadanda ake zaton ‘yan fashi da makami ne da kuma sauran ‘yan ta’adda a wasu sassan Jihar. “Mun farmaki maboyar masu aikata laifukan ne da duk wuraren da akwai alamar tambaya a kansu domin raba Jihar da masu aikata laifuka kwata-kwata,” in  ji Majiya.

Leave a Reply