GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

‘Yan bindiga sun saki Shugaban Bankin Noma da suka sace a harin jirgin ƙasa

Ƴan bindiga da suka kai harin bom a jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun saki shugaban bankin noma Alwan Ali Hassan ɗaya daga cikin fasinjojin da suka yi awon gaba da su a cikin jirgin.

An sake shi ne a ranar Laraba, kamar yadda wata majiya daga iyalinsa ta tabbatar wa BBC.

A ranar Litinin 28 ga watan Maris ƴan bindiga suka kai harin bom a jirgin ƙasa da ke kanyar zuwa Kaduna daga Abuja.

Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta ce jirgin na ɗauke da fasinja 362, kuma har yanzu ba a san makomar sama da 160 bayan tabbatar da mutum 182 da suka tsira.

Leave a Reply