Rahotonni daga jihar Filato da ke Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun sace wani basaraken kauyen Tal da ke karamar hukumar Pankshin.
BBC ta kalato dag Daily Trust cewa basaraken da aka sace shi ne Ngolong Tal, Alhaji Dabo Gutus. Lamarin ya faru ne misalin karfe daya na dare a ranar Litinin.
Wani mazaunin kauyen ya ce mutane na ta kokarin kiran ‘yan bindigar don sanin halin da basaraken yake ciki.
NAFDAC ta gargadi masu yin bilicin da su daina
Prince Dakup Ezra, wanda yake wakiltar kauyen Panshin a majalisar dokoki, ya yi kira a kwantar da hankali, yana mai cewa babban burinsu shi ne a kubutar da basaraken.
Ya yi kira ga mazauna masarautar da kuma yankin baki daya da su guji yin gaban kansu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.