BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

‘Yan bindiga sun kashe mutane a Masallaci a Zamfara

Akalla mutum 15 ne suka mutu, wasu kuma da dama suka jikkata a wani harin da a ka kai a wani masallaci a jihar Zamfara..

Kamfanin Dillacin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a Ruwan Jema da ke yankin karamar hukumar Bukkuyum a jihar, inda ‘yan bindigar a kan babura suka nufi masallacin a yammacin ranar Juma’a suka fara harbi kan-mai-uwa da wabi.

Harin na zuwa ne makonni uku bayan da aka sace wasu masallata a masallacin Zugu na karamar hukumar, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

A watan Yuli ma ‘yan bindigar sun kai hari a yankin tare da sace mutane da dama domin karbar kudin fansa.

Ana tsammanin dai ƴan bindigar na da sansani kusa da kauyen, abin da ya sa suke matsa ma wa yankin da hare-hare kenan.

Leave a Reply