Akalla mutum biyu ne ’yan bindiga suka harbe tare da yin awon gaba da wani dan kasuwa mai suna Nasiru Na’ayya a kauyen Gangarbi da ke Karamar Hukumar Rogo a Jihar Kano.
Wani ganau wanda dan uwa ne ga dan kasuwar ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki gidan Na’ayya ne da misalin karfe 12 na dare, suna ta harbe-hare.
Ya ce, “Da mutanen yankin suka yi yunkurin hana ’yan bindigar sace shi, sai suk aharbe mutum biyu, lamarin da ya kai ga mutuwar daya nan take, daya wani kuma ya samu rauni wanda a halin yanzu yana jinya a asibiti.”
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce a baya-bayan nan ne aka kai hare-hare Gangarbi da kauyukan da ke makwabtaka da su kamar Bari da Gwangwan.
Aminiya ta ruwaito cewa kauyen yana kan iyakar Jihar Kano da jihohin Kaduna da Katsina.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba shi da masaniyar faruwar lamarin, amma da zarar ya samu cikakken bayani zai sanar.