Kano Ayau Hausa, RAHOTANNI

Yadda ‘yan bindigar arewacin Najeriya ke samun makamai

Wani bincike da aka gudanar ya bankado cewa makaman da ake amfani da su a tashe-tashen hankula a jihohi uku na arewacin Najeriya sun fito ne daga kasashen Libya da Turkiyya da kuma Ivory Coast.

A cikin shekara uku, masu binciken daga cibiyar Conflict Armament Research sun tantance daruruwan bindigogi a jihohin Kaduna da Katsina da kuma Zamfara a Najeriyar, inda aka fi samun tashin hankali akai-akai tsakanin manoma da makiyaya.

Sun gano wasu makamai da aka kera a kasar Turkiyya na da alaka da wata kungiya da ba a bayyana sunansu ba, masu safarar makamai.

Kazalika sun gano wasu kananan bindigogi (assault rifles) daga kasar Iraki irin wadanda masu ikirarin jihadi suke amfani da su a yankin Sahel.

Wasu daga cikin makaman sun fito ne kai-tsaye daga rumbun makaman gwamnatin kasashen, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Kamanceceniya tsakanin makaman sun nuna cewa daga wuri daya ake samo su, sai dai cibiyar ta nanata cewa ba ta nufin ‘yan bindigar da ke kashe mutane a arewacin Najeriya suna da alaka da kungiyoyin ta’addanci.

An dade ana samun rikicin filaye a jihohin tsakiya da kuma arewacin Najeriyar, na shekaru da dama.

A shekarar 2018, kungiyar sasanta rikice-rikice ta duniya ta ce, yawan mutane da ake kashewa a rikice-rikice ya ninka sau shida fiye da na rikicin Boko Haram.

Leave a Reply