‘Yan bindigar da suka sace fasinjoji a jirgin kasar da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a Najeriya a watan Maris din da ya gabata sun saki karin fasinjoji biyar.
Hukumomin tsaro da gwamnatin kasar ba su tabbatar da sakin karin mutanen ba, amma gidan talbijin na Channels TV ya ambato mutumin da ke shiga tsakani domin sako fasinjojin Tukur Mamu yana cewa an saki mutanen ne a jiya Talata kamar yadda BBC ta kalato.
Ya bayyana cewa mutanen da aka saka su ne: Farfesa Mustapha Umar Imam, Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.
Gwamnati ta bayyana lokacin da jirgin kasan Kaduna-Abuja zai dawo
Babu bayani kan ko sai da aka biya kudin fansa kafin a saki fasinjojin.
A watan jiya ne aka saki karin wasu fasinjojin jirgin kasan na Abuja-Kaduna kwanaki kadan bayan ‘yan bindigar sun fitar da wani bidiyo wanda ya nuna su suna lakada musu duka.