BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Gwamnati ta bayyana lokacin da jirgin kasan Kaduna-Abuja zai dawo

Ministan Sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, ya ce tashohin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an dawo da waɗanda aka sace da iyalansu tare da samar da karin matakan tsaro.
Ya ce za a sayo kayan aikin tsaro na sa ido kan hanyoyin jiragen ƙasa.
Daily Trust ta rawaito cewa Ministan ya bayyana hakan ne bayan ya ziyarci tashar jirgin kasa ta Idu da ke Abuja a jiya Talata.
A cewarsa, “Kafin a sake bude tashohin jirgin, yana da matukar muhimmanci a samu ‘yan Najeriya da aka yi garkuwa da su sun dawo gida cikin iyalansu, in ba haka ba za a ga kamar gwamnati ba ta damu da halin da ƴan ƙasa ke ciki ba. Nan kuwa ba a san cewa gwamnati na yin duk abin da ya dace don ganin cewa wadanda wannan sace-sacen ya shafa sun dawo sun sadu da iyalansu.”
Na biyu, ya ce “dole ne a samar da isassun matakan tsaro da samar da kayayyakin tsaro don kariya da dakile duk wata barazana. Sauran abubuwa kuma sai mu barwa Ubangiji, amma mu za mu yi iya ƙoƙarin mu don ganin cewa an samar da cikakken tsaro a harkar sufurin jirgin kasan,” in ji shi.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a jiya Talatar ne dai ƴan ta’addan su ka sake sakin fasinjoji biyar da ga cikin waɗanda su ka yi garkuwa da su a harin da su ka kai kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a watan Maris.

Leave a Reply