Ɗaliban Kwaleji sun kashe ɗaliba bisa zargin kalaman ɓatanci ga Manzon Allah a Sokoto
Ɗalibai a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto sun kashe wata ɗaliba ƴar aji 2 a fannin tattalin arziki na gida bisa zargin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) a yau Alhamis.
Rahotanni sun baiyana cewa Ɗalibar, mai bin addinin Kiristanci, mai suna Deborah Yakubu, ta yaɗa kalaman ɓatancin ne ta Whatsapp ɗin makarantar.
Wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa wannan saƙo na ɓatanci ya jawo fushin ɗaliban, inda suka rinjayi a kan jami’an tsaron makarantar, su ka yi mata dukan tsiya har ta ce ga garinku nan, tare da banka wa gawarta wuta.
Daga baya jami’an hukumar sun rufe makarantar domin gudun kada lamarin ya ta’azzara.
“Bayan lamarin da ya faru na tarzomar dalibai da safiyar yau a Kwalejin, Hukumar Kwalejin ta yanke shawarar rufe makarantar har sai baba-ta-gani ba tare da ɓata lokaci ba.
“Saboda haka, an umarci dukkan ɗaliban da su bar harabar Kwalejin nan take,” in ji makarantar a cikin wata sanarwa.
Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa dalibar, inda ya yi kira ga hukumomi da su gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Rahotanni sun baiyana cewa tuni Gwamnatin Sokoto ta umarci a yi bincike kan lamarin