BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Yadda aka kashe Alex Badeh

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ‘yan bindiga sun kashe tsohon babban hafsan tsaron kasar Alex Badeh.

Sanarwar da kakakin rundunar Ibukunle Daramola ya fitar ranar Talata da daddare ta ce ‘yan bindigar sun kai hari kan motar da Mr Badeh ke ciki lokacin da yake kan hanyar komawa gida daga gonarsa a kan titin Abuja-Keffi.

A cewar sojin, tsohon babban hafsan tsaron na Najeriya ya mutu ne sakamakon raunukan da ya ji daga harbin bindigar da aka yi masa.

Tuni dai ‘yan kasar suka soma bayyana alhininsu kan kisan Mr Badex, cikin su har da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da takwaransa na majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Alex Badeh ya rike mukamai da dama na soji, ciki har da babban hafsan sojin sama da babban hafsan tsaron Najeriya.

A lokacin da ake tsaka da rikicin Boko Haram kuma yake kan mukamin babban hafsan tsaro, mayakan kungiyar sun kai hari a kauyensu, ViMtim da ke jihar Adamawa inda suka kona gidansa sannan suka kashe wani dan uwansa.

Ranar da ya yi murabus daga kan mukaminsa, Mr Badeh ya shaida wa manema labarai cewa rashin ingantattun kayan aiki ne ya yi musu dabaibayi a yakin da suke yi da kungiyar ta Boko Haram.

Sai dai a watan Fabrairun 2016, hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta zargi Mista Badeh da laifin satar kudi mallakin rundunar sojin sama ta kasar kimanin N3.9 bn, a lokacin da yake babban hafsan sojin kasar, domin sayen filaye.

EFCC ta ce Mista Badeh ya gina katafaren gida na kasaita har ma da rukunin shaguna a Abuja da wasu yankuna na kasar.

Mista Badeh dai ya musanta wannan zargi.

An haifi tsohon babban hafsan tsaron na Najeriya a shekarar 1957 kuma ya soma aikin soja a 1977.

Leave a Reply