Kano Ayau Hausa, Labarai

Ya kamata ‘yan fim su gyara-Adam A. Zango

Jarumi kuma mawaƙi a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango, ya yi wa ‘yan’uwan sa ‘yan fim matashiya kan wata magana da wani malami mai suna Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya yi a kan su a makon jiya.

Malamin ya saki wani gajeren bidiyo ne a soshiyal midiya inda ya kiran ‘yan fim ɗin Hausa da sunan marasa addini, kuma ya ce su na gudanar da haramtacciyar sana’a.

Maganar tasa ta harzuƙa wasu daga cikin ‘yan fim, inda har darakta Al-Amin Ciroma, da jarumi kuma mawaƙi Misbahu M. Ahmad su ka yi masa zazzafan martani.

A nasa bangaren, shi ma Adam A. Zango ya yi magana ne a wani bidiyo mai tsawon minti uku cif da ya wallafa a soshiyal midiya a yau Lahadi.

A bidiyon, wanda mujallar Fim ta kwafa, jarumin ya faɗa wa abokan sana’ar tasa cewa: “Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu ‘yan’uwa na ‘yan fim da kuma masoyan mu, ma’abota kallon finafinan mu da kuma sauraren waƙoƙin mu. Abubuwa sun cakuɗe game da wannan huɗuba da wannan malamin ya yi, ya harzuƙa ‘yan fim sosai, ran mu ya ɓaci.

“To amma magana ta gaskiya shi ne Bahaushe ya ce idan ɓera na da sata, daddawa ma ta na da wari; idan za mu gyara, mu gyara. Maganar gaskiya kenan,” kamar yadda muka kalato Nasara Redio.

Ya ci gaba da cewa: “Ni da kai da ku mun san inda ya ke da ɓuli ko in ce huji a cikin masana’antar mu, mun san inda ya ke a ɗinke. Ba yau aka fara yi mana wannan huɗubar a Jihar Kano ba, an yi mana wannan huɗubar da yawa, an yi addu’o’i a kan mu, an yi alƙunuti, kuma duk wannan abin da ake yi, yi ake yi wai don mu gyara. Amma ina! kowa ya na can ya na sabgar sa. Idan ka ga ‘yan fim sun haɗu cincirindo a wuri, to za a ba mu kuɗi ne ko kuma biki ne na ɗan’uwan mu ɗan fim, za mu zo mu caccashe a taka rawa, ko kuma mutuwa aka yi. Shi kan shi mutuwar idan ba babban jarumi ba ne ko babban furodusa ko babban darakta ya rasu, ba za ka ga cincirindon ‘yan fim ba, sai dai makusantar sa. Ka sani, na sani, kin sani!”

Zango ya ci gaba da cewa, “Aikin mu kullum shi ne mu je sitidiyo mu ɗauki hotuna, waɗanda su ka dace da wanda ba su dace ba, a zo a yi ta liƙawa a soshiyal midiya: wannan ya na ‘birthday’, waccan ta na ‘birthday’, duka a nan ake ganin mu. Ba za ka ji an ce ana Maulidi ga ‘yan fim ba, ana yin musabaƙa ko wa’azin ƙasa ko wani abu da ya shafi addini ko al’ada ba za ka gani ba.

“Amma maganar gaskiya shi ne manyan mu su na iyakacin ƙoƙarin su wajen ɗinke ɓaraka in ta tunkaro mu. Idan su ka kira mitin domin a zauna a tattauna a kan wani abu da zai iya jawo mana tashin hankali ko kuma jawo mana matsala cikin al’umma, wallahi ba za ka ga ɗan fim ba, a’a, sai dai su ya su su zauna su yi mitin ɗin da wasu ƙalilan wanda su ka amsa kira. Amma ba za ka ga musamman matan mu ba za ka taɓa ganin su a wurin da aka ce taron ‘yan fim ba ne yau za a yi a wuri kaza domin a ja hankalin su a kan wani abu da mutanen gari ko in ce masu kallon mu su ke ganin ba daidai ba ne, a gyara. Ba za ka gan su ba, ko in ce ba za ka gan mu ba.

“Amma dai kowa a cikin ‘yan fim su na da iyali, mata da ‘ya’ya, babban gida ko in ce malamai. Wasu ma iyayen su malamai ne sosai, wasu ma masu sarauta ne, da sauran su.

“To idan mu na tunanin cewa an san fuskar mu a duniya duk abin da mu ka yi za a kalla, to mummunan abin da mu ke aikatawa ma za a kalle shi a duniya – ko ka na so, ko ba ka so. Meye mafita? Mu gyara, faƙat.”

Leave a Reply