HANTSI, Kano Ayau Hausa

Ya kamata ministocina su yi alfahari da kansu – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa ministocinsa cewa ya kamata su yi alfahari da kasancewarsu wani bangare na “gwamnati mafi sanin makama”.

Shugaban ya bayyana haka ne a wajen taron majalisar ministoci ranar da ake yi duk ranar Laraba a fadarsa da ke Abuja.

Wannan dai shi ne zaman da shugaban ya yi a majalisar zartarwarsa na karshe da ministocinsa.

Sai dai shugaban ya ba su damar ci gaba da aiki har zuwa 28 ga watan Mayu, inda za su mika takardar ajiye aiki ga sakataren gwamnati Boss Mustapha, kwana daya kafin a rantsar da sabuwar gwamnatinsa a mako mai zuwa.

Da yake jawabi a cikin dakin taron, Shugaba Buhari ya ce sunayen ministocin ya shiga cikin tarihin Najeriya, wanda hakan abin alfahari ne.

“Kowannenku yana da wata baiwa ta musamman kuma mu ne hoton Najeriya da muke fatan ginawa. Kasa mai kabilu da dama wadda kowanne dan kasa yake da ‘yancin fadar albarkacin bakinsa.

“Ya kamata ku yi alfahari da kasancewarku wani bangare na gwamnnatin da kwato wasu kananan hukumomi daga hannun ‘yan Boko Haram.

“Ku yi alfahari da gudummawar da kuka bayar wajen samar da abinci da kuma shirin gwamnatinmu na habaka tattalin arziki, wanda ya sa Najeriya ta fita daga mummunan matsin tattalin arziki a cikin shekaru da dama da ta shiga.

“Ku yi alfahari da shirye-shiryen da kuka bullo da su, wadanda suka habaka jin dadin miliyoyin ‘yan Najeriya.” kamar yadda BBC ya ruwaito

“Lallai ya kamata ku yi alfahari da aikinku na samar da ayyukan da babu kamarsu a tarihin Najeriya na tituna da layin jirgin kasa da kuma gyaran filayen jirgin sama.”

Bayanan shugaban ba su nuna cewa ko zai ci gaba da sabuwar gwamnatin da wasu daga cikinsu ba.

Leave a Reply