An kama wani mutum mai suna Adewale Lukmon, da ake zargi da hada baki da abokansa Bidemi Fatai da Saheed Owolabi da Babatunde Ageele suka yi wa uwargidansa Funmilayo fashin Naira dubu 159.
Ma’auratan suna zaune a gida daya ne a rukunin gidaje na Eruwen da ke Ikorodu a Jihar Legas. Wata majiya ta ce Funmilayo ta samu kudin ne a wata kwangilar gine-gine da take yi a ranar 23 ga watan Yulin bana. Adewale ya raka matar tasa Funmilayo zuwa banki don ajiye kudin amma aka dawo da ita saboda ba ta da rajistar lambar BBN. Sai suka koma gida da kudin
Kuma da suka koma gida sai matar ta fita da kudin, yayin da mijin ya fita da abokansa.Sai dai daya daga cikin abokansa, wato Fatai ya dawo gidan da misalin karfe 10 na dare bisa zaton Funmilayo ta ajiye kudin a gidan. Kuma yana cikin bincikar inda ta ajiye kudin ne sai Funmilayo ta dawo tare da kudin.
Rigima ta kaure a tsakaninsu inda wanda ake zargin ya kwace kudin ya gudu.
Kuma ta sanar da ’yan sanda inda suka kama wanda ake zargin.
A lokacin da ’yan sandan suke tuhumar Fatai ne ya ambaci suna mijin matar da sauran masu hannu a aika-aikar. An gurfanar da su a Kotun Majistare ta Ikorodu bisa zargin hadin baki da kwace da fashi da makami.
Takardar kara a kotun ta ce: Adewale Lukmon da Bidemi Fatai da Saheed Owolabi da Babatunde Agele da sauransu, a ranar 23 ga watan Yuli da misalin karfe 10 na dare a rukunin gidaje na Leadway da ke Erunwen a Ikorodu, da ke karkashin hurumin Kotun Majistare ta Ikorodu, kun hada baki kuka nuna karfi kuka aikata fashi don haka kukn aikata laifin da za a hukunta ku a karkshin dokar manyan laifuffuka ta Jihar Legas ta shekarar ta 2015, sashi na 299 na dokar aikata laifi. Kotun dai ta bayyana wadanda ake zargin da cewa sun yi yunkurin yi wa Funmilayo fashin Naira dubu 159.
Sai dai wadanda ake zargin ba su amince da zargin da kotun ke yi musu ba. Kuma an bai wa wadanda ake zargin beli a kan Naira dubu 100 kowannensu tare da gabatar da mutum biyu da za su tsaya musu. An kuma dage sauraran shari’ar zuwa 11 ga Oktoban nan.