BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Wani maniyyaci ya yi aikin Hajjinsa a Kano

Wani maniyyaci mai suna Jibrin Abdu daga ƙaramar hukumar Gezawan jihar Kano, ya aiwatar da aikin Hajjinsa a hukumar tattara alhazai ta jihar Kano, bayan sun sha rana da sanyi amma tafiya ba ta samu ba.

Malam Jibrin, wanda aka gan shi sanye da hiraminsa, ya bayyana cewa ya yi Safa da Marwa ya yi Sa’ayi kuma a shirye yake domin ƙarasa sauran ayyukan aikinsa. Malam Jibrin ya ce yana fatan Allah ya ba shi ladan wannan aikin da ya yi saboda kyakkyawar niyyarsa kamar yadda muka kalato daga The Daily Reality Hausa.

Da yake zantawa da manema labarai, Malam Jibril ya ce gonarsa ya sayar don ya yi wannan aiki, amma kuma haka ta zo ta faru a kamsa

Maniyyacin ya ce matan 4 tare da ‘ya’yansa 27, kuma bai ci bashin kowa ba. Da kuɗinsa da ya sayar da gonarsa ya biya miliyan 1 da dubu ɗari 2 a karon fari, sannan yana da dukkanin rasitan biyan duk kuɗin da ya biya.

Malam Jibrin ya yi kira ga maniyyatan da ba su sami damar tashi ba da su yi haƙuri su dangana saboda yanayin da suka tsinci kansu a ciki. Yayi kira ga maniyyatan da kar su yi wa kowa yarfe, su ɗauka wannan al’amari ne daga Allah.

Idan za a iya tunawa an sami dambarwa mai ƙarfi tsakanin gwamnatin Kano da jirgin Azman wanda wasu suke ganin hakan yana daga cikin dalilan matsalar.

Leave a Reply