Kano Ayau Hausa, Labarai

Tsarin taƙaita cirar kuɗi na CBN zai magance maguɗin zaɓe — Sarki Sanusi

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, kuma mai martaba Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su firgita kan sabuwar manufar da babban bankin ya bullo da shi na takaita fitar da kudade.
Malam Sanusi, wanda ya ce jama’a sun masa tambayoyi kan ra’ayinsa a kan lamarin, ya bayyana cewa sabuwar manufar za ta shafi ‘yan siyasa ne kawai wadanda suka tura makudan kudade domin yin magudi da kuma kawo cikas ga tsarin zaben.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da karatun mako-mako a shafinsa na Facebook.
Ya kuma shawarci ‘yan Nijeriya, musamman talakawa da kada su bari ‘yan siyasa su yaudare su da kalaman yaudara don su tausaya musu su zaɓe su.
“Idan za ku iya tunawa, wannan ba sabuwar manufa ba ce; manufa ce da na bullo da ita a lokacin da nake gwamnan CBN. A cikin 2012, mun gabatar da wata manufa mai suna “Cashless Nigeria,” kamar yadda muka kalato daga Daily Nigerian Hausa.
“Kuma mun fara ne a Legas, daga baya kuma a jihohi biyar da FCT.
“Dalilin mu shine saboda duniya na tafiya da hanyar sadarwa ta zamani, an wuce amfani da tsabar kudi. Don haka mun so a sassauta hada-hadar kudi a kasar.
Malam Sanusi ya kara jaddada cewa manufar za ta bai wa bankunan damar bin diddigin asusun ajiyar kudaden da aka wawashe cikin sauki.
“Don haka wannan sabuwar manufa ta CBN za ta rage wa wadannan kura-kurai a zaben.
“Saboda ko kuna son ba wa jami’an tsaro cin hanci, ko INEC, ko alkalai su yi maku magudin zabe, za ku biya ta asusun ajiyarsu na banki, kuma za a iya gano kudaden cikin sauki.
“Dimokradiyyarmu ta bai wa ‘yan kasa damar zaben ‘yan takarar da suka ga dama, ba wai wanda mai karfi ne da zai wawure baitul mali ba,” inji Sanusi.

Leave a Reply