Kano Ayau Hausa

Tinubu ya dauki Kashim Shettima a mataimakinsa

Dan takarar shugabancin ƙasar Najeriya a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya zaɓi Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai masa mataimaki.

Ɗan takarar shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a yau, yayin wata ziyarar barka da sallah da ya kai wa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Daura.

A watan da ya gabata ne dai Tinubun ya ayyana Ibrahim Masari a matsayin mataimakinsa, inda tun a lokacin masana siyasar ƙasa suka masa laƙani da mataimakin riƙo.

Leave a Reply