Da ya yi yunkurin shiga Makka don rushe Ka’aba sai Allah (SWT) Ya aiko da wasu tsuntsaye dauke da kananan duwatsu na wuta, suka yi ta jefa musu wadannan duwatsu guda-guda, kuma nan take suka hallaka Abrahata tare da rundunarsa. Allah (SWT) Ya ba mu labarin abin da ya faru da Abrahata da jama’arsa a cikin Alkur’ani Mai girma, Yana cewa:
“Ashe ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba? Ashe bai sanya kaidinsu a cikin bata ba? Kuma Ya sako bisa kawunansu wasu tsuntsaye, gungu-gungu. Suna jifar su da wasu duwatsu na yumbun wuta. Sa’annan Ya sanya su kamar wani karmami wanda aka cinye?” (Suratul Fil: 1-5).
Daga wannan karo ne Larabawa suka kara ganin martabar wannan Daki Mai tsarki. Haka dukan yankin Larabawa da kananan kabilunsu suka kara girmama garin Makka da wannan Daki Mai alfarma na Ka’aba. Ziyara don zuwa Ka’aba ta karu, suka kuma sanya gumaka wajen 360 a dakin don neman su kara kawo su kusa da Allah.
A wannan shekarar ce da Larabawan Makka suka ga abin al’ajabi, cikin watan Rabi’ul Auwal wato shekara ta 570, Miladiyyar Annabi Isa (AS) aka haifi Farin Jakada Annabinmu Muhammad (SAW) a wannan gari na Makka. Garin da Allah (SWT) Ya arzurta shi da baiwarSa Ya sanya mazaunin DakinSa a wurin Ya kuma sanya AnnabinSa Isma’il (AS) ya tashi cikinsa, ya rayu cikinsa kuma ya rasu cikinsa. Kuma a cikin tsatsonsa ne aka samu zuriyar Shugaban Manzanni, Manzon Tsira Manzon Rahama, Cikamakin Annabawa Annabi Muhammad (SAW).
Darasi na Hudu
Haihuwar Manzon Allah (SAW):
An haifi Manzon Allah (SAW) ne a Kwarin Bani Hashim a ranar Litinin 8 ko 12 ga watan Rabi’ul Auwal, Shekarar Giwa. 8 ga watan shi ya fi inganta, 12 ga wata kuma shi ya fi shahara. Malamai sun yi sabani kan haka:
Wadansu kuma suka ce 2 ga watan, wadansu kuma 8, wadansu kuma 10, wadansu kuma suka ce 12 ga watan. Babban Malamin Tafsirin nan Ibn Kasir, ya ce: “Maganar da babu sabani a kai ita ce cewa: An haife shi ne shekarar da ake kira Shekarar Giwaye kamar yadda Ibrahim Ibn Al-Munzir Alhuzami, Malamin Bukhari da Khalifatu Ibn Khayya da sauransu suka fada.” Mahaifin Annabi (SAW) ya rasu ne kafin a haife shi. Annabi (SAW) an haife shi a ranar 22 ga watan Afrilu 571 Miladiyar Annabi Isa (AS). Shifa’u ’yar Amru uwar Abdur-Rahman bn Auf ita ta karbi haihuwarsa. Bayan haihuwarsa sai Amina ta aike wa kakansa Abdulmuddalib da bushara. Abdul-Muddalib ya taho cike da farin ciki, ya dauki Annabi (SAW) ya shigar da shi Ka’aba yana mai godiya ga Allah kuma ya sanya masa Muhammad don ya zama abin yabo, ya ciyar da mutane ranar bakwai kamar yadda al’adar Larabawa take a lokacin.
Darasi na Biyar
Dangantakar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) da tsatson Annabi Ibrahim (AS):
Annabi Ibrahim (AS) ya rayu cikin al’ummarsa lokaci mai tsawo yana yi musu gargadi don su kadaita Allah wajen bauta. Ya gamu da jarrabawa mai yawa, kuma kamar yadda malaman tarihi suka nuna, a wannan tsawon lokaci da ya kira mutanensa babu wadda ya amsa kiransa face dan uwansa Annabi Lut (AS) da matarsa Saratu. Ana cikin wannan ne sai Annabi Ibrahim (AS) ya yi hijira zuwa Haran (da ke kasar Sham), sannan zuwa Kan’an (kasar Palasdinu) daga bisani ya tafi kasar Masar, inda ya hadu da sarkinsu na wancan zamani wanda ya yi wa Saratu kyautar wata baiwa mai suna Hajara. Alkur’ani Mai girma ya ba mu labarin yadda Allah (SWT) Ya kubutar da shi daga hannun Lamarudu Ya kuma umarce shi da yin hijira (daga Babila zuwa Sham), inda Allah (SWT) Yake cewa:
“Kuma suka yi nufin wani mugun shiri a gare shi, sai Muka sanya su mafiya hasara. Kuma Muka tserar da shi, da Lut zuwa ga kasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga talikai” (Anbiya:70-71)
A lokacin da Annabi Ibrahim (AS) ya dawo kasar Palasdinu sai ya auri Hajara, wadda hakan ya jawo kishi daga matarsa Saratu. Wannan kishi ya kara tsananta a lokacin da Hajara ta haifa wa Annabi Ibrahim (AS) da namiji, musamman ganin ita Saratu ba ta taba haihuwa ba. Wannan ya sanya Annabi Ibrahim (AS) ya dauki Hajara da jaririnta zuwa wani wuri cikin kwazazzabon Makka, inda ya bar Hajara da karamin danta Isma’il a wannan wuri babu kowa kuma babu abinci babu ruwan sha. Hajara ta tambayi Annabi Ibrahim (AS) dalilin barinsu a wannan wuri, ta ce, “Allah ne Ya umarce ka da ajiye mu a nan?” Ya ce, “Eh, da ishara. Don haka ta amince da wannan umarni na Ubangijinta tare da samun karfin gwiwa cewa Allah Yana tare da su.
Bayan tafiyar Annabi Ibrahim (AS) sai bukatar ruwa ta bijiro wa Hajara. Ruwan shansu ya kare kuma babu wata hanya ta samun ruwa gare su. Saboda haka ta rika tafiya daga dutsen Safa zuwa dutsen Marwa, tana neman wurin da za ta samu ruwa. Bayan ta je zuwa ga Safa sau bakwai, ta je Marwa sau bakwai, sai Allah (SWT) Ya aiko Mala’ika Jibril (AS) ya samar musu da rijiyar Zamzam a dab da inda suke zaune. Don haka suka samu isasshen ruwa domin amfaninsu. Samun ruwa a wannan wuri ya kawo musu albarka tare da jawo mutane wannan wuri da babu wani dan Adam da ke zaune a cikinsa. A bisa haka ne, wata rana wadansu matafiya cikin kabilar Kahdan da ke kasar Yamen suka zo wucewa kusa da wurin, sai suka hangi tsuntsaye suna shawagi, ganin haka suka ce lallai a wancan wuri ba za a rasa ruwa ba, sai suka karasa wurin kuma suka tarar da ruwan rijiyar Zamzam tare da Hajara da danta Isma’il, a wannan wuri da ke kusa da Dakin Ka’aba.
Zuwan wadannan mutane ya jawo karin wadansu mutane daga Yamen daga cikin kabilar Jurhum, wadanda suka tare a wurin. Kuma Isma’il ya rayu cikinsu ya kuma koyi harshen Larabci a wurinsu. Bayan haka, Isma’il ya auri mata biyu a cikin kabilar Jurhum, wadda daya daga cikinsu ta kasance ’yar Muddad Ibn Amr, jagoran kabilar Jurhum.
Daga baya, Isma’il tare da mahaifinsa Ibrahim (AS) sun gina Dakin Ka’aba tare da yin addu’o’i don neman albarka ga garin Makka. Ya kuma rayu a wannan wuri, bisa maganar malaman tarihi, har tsawon shekara 137, inda ya bar ’ya’ya goma sha biyu, wadanda suka haifar da kabilu goma sha biyu, wadanda wadansu daga cikinsu suka rayu a kasar Makka, wadansu kuma suka warwatsu a sauran kasashe.
A cikin wadannan kabilu goma sha biyu akwai manya guda biyu, wato kabilun Nabat da ta Kaydar, wadanda suka fi sauran shahara. Kabilar Nabat sun bar garin Makka sun kafa tasu daular a wani wuri, lokacin da ita kuma kabilar Kaydar ta rayu cikin garin Makka, ta baza rassanta har zuwa tsatsonta na talatin da takwas inda zuriyar Adnan ta samu tushe. Annabi Muhammad (SAW) ya fito ne daga gidan Banu Hashim a cikin kabilar Kuraishawa, wadda daya ce daga cikin zuriyar Adnan.
Za a iya samun Aliyu Muhammad Sa’id, Gamawa
Ta +2348023893141. Email: aliyugamawa@gmail.com