FITATTUN MATA, Kano Ayau Hausa

Takaitaccen Tsokaci A Kan Interfaith Dialogue

Daga Farfesa Salisu Shehu
Ta hanyar Interfaith Dialogue (Hiwaru Adyan) ne Shari’ah ta tabbata a Constitution din Nigeria. Na ga ‘yan uwana almajirai, a dalilin rashin fahimtar turanci da kuma rashin sanin cikakken tarihin Nigeria, har cewa suke wai Interfaith Dialogue kafirci ne. Duk da Malamanmu kamar Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo da Professor Mansur Sokoto sun yi bayani cewa akwai banbanci tsakanin Interfaith Dialogue (Hiwarul Adyan) da Unification of Religions (Wahdatul Adyan) amma na lura da yawa sun kasa fahimtar wannan banbanci. Suna hakikancewa wai Interfaith shi ne “shigar addini cikin wani addini”.
Wanda duk ya ce wai Interfaith Dialogue bashi da wani anfani ga Musulmi, to sai mu ce masa watakila yana da nakasu/gibi a saninsa ga tarihin Nigeria.
Sai da aka yi zazzafar muhawara tsaknin Musulmi da Kirista a Constitutional Assemly a shekarar 1978, har kamar za a yi kutufo tsakanin juna tsakanin Musulmai da Kafirai a kan Shari’ah kafin aka tabbatar da Shari’ah a Constitution din Nigeria. Tsayuwar daka da Musulmai suka yi babu tsoro, da kuma nuna babu gudu, babu ja da baya da kuma kwararan hujjoji da Musulmai suka gabatar akan cewa idan ana son zaman Nigeria a matsayin kasa daya dunkulalliya dole a tabbatar da Shari’ah ga Musulmai a cikin Constitution din Nigeria. Da wannan ne Allah Ya taimaka suka yi galaba akan Kiristoci aka tabbatar da Shari’ah a 1979 Constitution.
A dalilin tabbatar da Shari’ah a 1979 Constitution ne Allah Ya taimaka da aka zo bitar Constitution a Shekarar 1999 Shari’ah ta kara tabbata daram, daram dam dam daram. Amma shi ma sai da aka kai ruwa rana a muhawara tsakanin Musulmai da Kiristoci a National Constitutional Conference na 1995/1996.
Wannan tabbatuwar Shari’ah a Constitution din Nigeria ta hanyar muhawara tsakanin Musulmai da kafirai shi ne ya zamanto Babbar majingina ko madogara da Excellency Ahmad Sani Yariman Bakura lokacin da ya kuduri aniyar fadada Shari’ah a shekarar 2000. Kuma a videon da ya yi ta yawo kwanan nan an ji yanda aka yi muhawara da Shugaban Kasa na wannan lokacin Obasanjo da sauran kiristoci akan Shari’ah. Dole suka hakura saboda kokarin da Musulmai suka yi a baya wajen tabbatar da ita a Constitution din Nigeria.
Kuma bayan fadada Shari’ah a Jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa kafirai sun ci gaba da yakarta ta kafafe daban – daban. { یُرِیدُونَ أَن یُطۡفِـُٔوا۟ نُورَ ٱللَّهِ بِأَفۡوَ ٰ⁠هِهِمۡ وَیَأۡبَى ٱللَّهُ إِلَّاۤ أَن یُتِمَّ نُورَهُۥ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَـٰفِرُونَ }
[سُورَةُ التَّوۡبَةِ: ٣٢]
Allah Shi ne shaida a kan fafatawar da muka rinka yi a dandaloli na Interfaith Dialogue musamman a tsakanin Abuja da Kaduna da Jos da sauran wurare wajen muhawara da kiristoci a kan Shari’ah, musamman Hisbah da dai sauransu.
Idan wannan shi ne kafirci kamar yanda akasarin masu wa’azi suke fada, to ina kiransu da su fadada tinani, su zurfafa bincike a kan ma’anar Interfaith Dialogue da kuma abubuwan da ta kunsa.
Hakika abinda ya wajaba akanmu Musulmai shi ne mu yi ta’asilin manufofinmu, da ka’idodinmu, da matakanmu, da fuskoki da fajjojinmu na yin muhawara da kafirai a bisa koyarwar Al-Qur’ani da Sunnah kamar yanda Professor Mansur da Professor Dogarawa suka yi kokarin tabbatarwa a bayanansu da rubuce-rubcensu. Sa’annan kuma mu tsaya mu yi kyakkyawan tsari wajen tabbatar da cewa ba kowane Musulmi ne zai je ya shiga Interfaith Dialogue ba sai wanda yake da Ilimin Musulunci mai zurfi. Akalla a tabbatar yana da ahliyya ta zazzago nassoshin Qur’ani da Sunnah ba tare da lahani ko rudani ba. Kuskure ne namu gaba daya da muka bar mutanen da suke “wala yakadu yubin” a Qur’ani suna zuwa suna wakiltarmu a fagagen Interfaith Dialogue.
Wallahi, a Kasa irin Nigeria inda ake da al’ummai mabanbanta addinai, akidu da kabilu, da al’adu ba karamin kuskure bane a ce wai kada Musulmai su yi muhawara ta addini da kafirai.
Misalai na yanda muhawara tsakanin Musulmai da kafirai suka tabbatar ma Musulmai nasarori a kan addini da rayuwa suna da yawa. Daga ciki akwai canja suturar mata Nurses Musulmai. Duk dan shekara 50 ya san yanda Nurses Musulmai suke fita tsirara. Amma muhawara da karfn hujjar Musulmai suka sa yau gashi nurses dinmu Musulmai suna sanya Hijabi. Wannan ya taimaka wajen kwadaitar da iyaye su rika barin ‘ya’ yansu Musulmai su karanci fanning Nursing.
Ni dai na lura da yawa daga cikin wadanda suka yi kuskuren cakuda Interfaith Dialogue (Hiwarul Adyan) da kuma Unification of Religions (Wahdatul Adyan) basu yi mura’atin ayar nan ta Suratul Isra’i ba:
{ وَلَا تَقۡفُ مَا لَیۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولࣰا }
[سُورَةُ الإِسۡرَاءِ: ٣٦]
Kuma sunki su yi aiki da ayar Suratun Nahli:
{ وَمَاۤ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالࣰا نُّوحِیۤ إِلَیۡهِمۡۖ فَسۡـَٔلُوۤا۟ أَهۡلَ ٱلذِّكۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ }
[سُورَةُ النَّحۡلِ: ٤٣]

Leave a Reply