FITATTUN MATA, Kano Ayau Hausa

Tinubu Ya Haramta Wa Ministocinsa Fita Ƙetare

Shugaba Bola Tinubu ya haramta wa ministoci da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati tafiye-tafiye zuwa ƙetare daga yanzu zuwa tsawon watanni uku.

Shugaban ma’aikata a fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da umarnin cikin wata takarda da aka aike wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.

Sanarwar ta bayyana ƙalubalen tattalin arzikin da ake fama da shi da buƙatar alkinta kuɗin gwamnati da ake kashewa yayin irin waɗannan tafiye-tafiye a matsayin dalilan da suka sa aka ƙaƙaba haramcin wucin-gadi kan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.

Takardar ta ce duk wani jami’i na buƙatar amincewar shugaban ƙasa idan yana son a ɗage masa haramcin kuma dole a yi hakan mako biyu kafin lokacin tafiyar.

Ofishin ya gudanar da wani taron ƙarawa juna sani a birnin Landan wanda ya samu halartar kwamishinonin kuɗi da jami’ai daga Ofishin Akanta-Janar.

Aminiya ta ruwaito cewa, an dai gudanar da taron ƙara wa juna sanin ne Otel din Copthorne Tara da ke Kensington a Landan daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Maris.

’Yan Najeriya dai sun yi ta tsokaci a kai, abin da suka ce ya zo ne a lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da kuma tashin dala da ke shafar darajar kuɗin naira.

Leave a Reply