Kano Ayau Hausa, Labarai

Sojojin Najeriya sun gano ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok

Rundunar sojin Najeriya ta gano ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok a Jihar Borno.

A wani saƙo da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce dakarun rundunar haɗin gwiwa ta 26 ne suka gano ta a lokacin da suke shawagi a kusa da garin Ngoshe a jiya Talata.

Sojojin dai sun ce sun ga Mrs Mary Ngoshe ne ɗauke da ɗanta kamar yadda suka wallafa hotonsu a shafinsu na Twitter kamar yadda BBC ta kalato.

Tun a Afrilun 2014 ne dai aka sace sama da ƴan matan na Chibok 270 sai dai sama da 100 an sako su wasu kuma sun tsere.

Leave a Reply