Rundunar Soji ta Uku da ke Jos a Jihar Filato ta kama mutum 30 da ake zargi da hannu wajen bacewar Manjo Janar Muhammad Idris Alkali (mai ritaya).
Wata majiyar soji ta bayyana wa Aminiya cewa mutanen da aka kama suna tsare a barikin sojoji na rundunar da ke Jos.
Majiyar ta kara da cewa, “Sojoji sun fara aikin kama mutane a Gundumar Du da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a safiyar shekaranjiya Laraba, kuma aikin ya samu nasara inda aka kama mutum 30 da ake zargi da hannu wajen bacewar Manjo Janar Alkali.
A cikin sakon da Mataimakin Babban Daraktan Labarai na Rundunar taUku, Kanar Kayode Ogunsanya ya turo wa Aminiya, ya tabbatar da kama mutanen da ake zargi da hannu wajen bacewar Manjo Janar Alkali.
Sai dai ya ki ya bayyana adadin mutanen da aka kama din. Ya ce, “Abu ne da aka saba duk lokacin da aka tashi bincike a kama mutane, a yanzu haka mun kama wadansu mutane, muna gudanar da bincike, a yanzu haka dai mun kawo su barikin sojojin runduna ta uku don ci gaba da bincike.”
Da aka tambaye shi adadin mutanen da aka kama sai ya ce, “A yanzu ba zan iya sanin adadin mutanen da aka kama ba.”