BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Sojoji na samun cikas a kokarin ceto fasinjojin jirgi kasa – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ‘yan bingigar da sukan sace fasinjoji a wani jirgin da ke kan hanyarsa daga Abuja zuwa Kaduna dake arewacin kasar su na amfani da farar hular da suka sace a matsayin garkuwa, lamarin da ke kawo cikas ga sojojin da ke kokarin kwato su.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa, wadda ake caccaka da rashin yin abin a – zo – a- gani wajen kwato mutanen da aka sace tana kokari ne ta kauce wa mummunan sakamako, duba da cewa duk wani aikin ceto da zai zamo sanadiyyar mutuwar wadanda ake kokarin kubutarwa ba alkhairi bane.

A makon da ya gabata kafofin yada labaran Najeriya suka nuno wani bidiyo na wadanda aka sace, ciki har da wani jariri da daya daga cikin wadanda ake garkuwa da su ta haifa.

Hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya ta ce mutane 168 new suka bace biyo bayan harin da aka kai wa jirgin a ranar 28 ga watan Maris.

Satar mutane ta zama ruwan dare a Najeriya, inda ‘yan bindiga da suka kafa sansanoni a dazukan kasar suke daukar mutane don karbar kudin fansa.

Leave a Reply