GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Shugaban Otel din Tahir da ke Kano ya rasu

Fitaccen ɗan Kasuwar nan na Kano Tahir-Fadlallah ɗan asalin ƙasa Labanon, kuma mamallakin Otal ɗin Tahir Guest Palace ya rasu, yana da shekaru 74 a Duniya.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan ta shafinsa na Facebook.

Kafin rasuwarsa shi ne Shugaban ƴan ƙasar Labanon mazauna Kano.

Ya rasu ne a kasarsa Lebanon, amma a Kano za a binne shi.

Leave a Reply