Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi magana ta waya da mahaifiyar Leah Sharibu, Misis Rebecca Sharibu a shekaranjiya Laraba.
Leah, dalibar makarantar sakandaren GGSTC Dapchi a Jihar Yobe, ’yan Boko Haram ne suka kama ta tare da ’yan uwanta dalibai mata a ranar 19 ga Fabrairun da ya gabata, inda suka sako sauran daliban, ita kuma suka ci gaba da rike ta har zuwa yanzu bisa hujjar cewa ta ki canja addininta daga Kiristanci zuwa Musulunci.
A watan Agustan da ya gabata, an samu bullar wani faifan magana, inda aka ji Leah tana magana da Hausa, tana rokon hukumomi su taiumaka mata a ceto ta daga ’yan Boko Haram.
Fadar Shugaban Kasa, ta bakin Kakakin Shugaban, Garba Shehu, ta ce a tattaunawar da Shugaban Kasa ya yi da mahaifiyar Leah, ya ba ta hakuri tare da karfafa mata gwiwa, cewa gwamnati za ta yi iya kokarinta wajen ganin an maido mata da ’yarta gida.
“Ina taya ku jimami kuma ina kara nanata muku cewa gwamnatinmu da sauran al’ummar kasa suna taya ku jimami. Kuma muna nan muna matukar kokarin ganin cewa an dawo da ita da rai kuma cikin koshin lafiya,” inji Shugaba Buhari.