Dan majalisar wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni a jihar Kano, Shaaban Ibrahim Sharada, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADP.
Bayan sauya sheka, DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa dan majalisar ya koma jam’iyyar ADP kuma ya karbi tikitin takarar gwamna na jam’iyyar.
Majiya mai tushe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC da ke Kano, ta ce Sharada zai yiwa jam’iyyar ADP takara tare da abokin takararsa, Rabiu Bako.
Sharada wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro da leken asiri, ya yi takarar neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC amma mataimakin gwamnan jihar Nasiru Gawuna ya kayar da shi.