Kano Ayau Hausa, Manyan Labarai

Saudiyya ta dakatar da aikin Umara saboda Cutar Kurona

Saudiyya ta sanar da hana maniyatta aikin Hajji da Umrah shiga biranen Makkah da Madina, a wani matakin hana yaduwar cutar coronavirus mai shafar numfashi.

Ma’aikatar harkokin waje ta Saudiyya ta kuma ce za ta hana ‘yan kasashen da aka tabbatar akwai cutar ko tana barazana ga kiwon lafiyar al’umma zuwa kasar.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ta wallafa a Twitter ta kuma ce ta dakatar da amfani da katin shaidar dan kasa maimakon fasfo lokacin shiga da fita daga Saudiyya, kamar yadda BBC ta kalato.

A ranar Laraba Iraqi ta haramta gudanar da ko wane irin nau’in taruka na jama’a, da kuma kulle makarantu da jami’o’in kasar har da wuraren shakatawa saboda fargabar bazuwar a yankin Gabas ta Tsakiya.

Tuni kasashen Oman, da Kuwait da Bahrain suka dauki irin wadannan matakan, bayan da aka tabbatar da bayyanar cutar ta covid-19 a kasashen.

Kasashen sun kuma tabbatar da cewa wadanda suka kamu sun shiga kasashen ne daga Iran inda cutar ke habaka fiye da ko ina a wajen China.

Dakatar da mahajjata zuwa Saudiyya na zuwa ne kwana 60 kafin a soma azumin watan Ramalana. Watan azumin shi ne lokaci mafi cunkoso da miliyoyin masu Umrha ke kai ziyara kasar ta Saudiyya.

Leave a Reply