Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya ya nada dansa kuma Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ga mukamin firaministan kasar sannan ya nada dansa na biyu Yarima Khalid a matsayin ministan tsaro, kamar yadda wata dokar da Sarkin ya sanya wa hannu ta sanar.
Sauyin ya kuma bar Yarima Abdulaziz bin Salman a matsayinsa na ministan makamashi.
Ministan harkoki da kasashen waje Yarima Faisal bin Farhan al Saud da ministan kudi Mohammed al-Jadaan da kuma ministan zuba jari Khalid al-Falih sun ci gaba da rike mukamansu.
Yarima Mohammed bin Salman, wanda aka fi sani da MBS a baya ya rike mukamin ministan tsaro kuma shi ne ke tafiyar da mulkin kasar ta Saudiyya.
Dokar ta kuma ce Sarki Salman ne zai rika jagorantar tarukan majalisar ministocin kasar da ya halarta.
Pingback: Majalisar Wakilai ta bukaci a dawo aiki a hanyar Kaduna-Abuja - Kano Aya uKano Aya u