Sarkin Zamfaran Anka, kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Attahiru Ahmad ya ce talakawa marasa karfi ne suka fi yawaita aure maimakon masu hali da ya kamata su rika karawa.
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron bikin cika shekara 50 da kafa Sashin Nazarin Kimiyyar Siyasa da Hulda da Kasashen Waje na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Sarkin ya ce wannan dabi’a ce wadda ta yi sanadiyyar rasa aiki ga daya daga cikin masu yi masa aiki, inda ya kore shi bayan ya kara auren mata ta uku.
Ya bayyana cewa a lokacin da ya dauke shi aiki a bisa tausayawa yana da mata biyu kuma albashinsa Naira dubu bakwai ne, amma sai ya kara auro mata ta uku. Saboda haka ya sallame shi daga aikin, domin bai shirya yin adalci ba ga iyalansa.
Sarkin ya koka kan yadda tarbiyya da dabi’un ’yan Najeriya suke komawa baya a kullum. Ya nuna takaicinsa kan yadda a kullum ake kwaikwayon rayuwar Amurkawa da dabi’unsu da kuma salon mulkinsu, wanda sam bai da ce da Najeriya ba. A cewarsa, “Mun yi sakaci inda muka yi watsi da dukan al’adunmu da tarbiyarmu da kuma salon mulkin da muka gada, wanda shi ne ke rike da hidimominmu na yau da kullum.”
Alhaji Attahiru ya kuma koka kan yadda ake yi wa masu mulki da shugabannin al’umma bita-da-kulli da munafunci da hassada da kuma keta, domin kada su samu nasarar tafiyar da mulki. A cewarsa, “Hakan ne ya yi sanadiyar yin hijirar wadansu malamai daga kauyuka zuwa birane tare da dibar almajirai wadanda kuma su ne ke yin barace-barace don neman abinci, wanda haka ya saba wa tarbiyyar da aka sanmu da ita.”
Ya kuma yi nuni da irin hadarin da ke tattare da yawan barace-baracen yara, musamman a wannan lokaci da harkar tsaro ta tabarbare, inda akan samu marasa kishi su yaudari matasan, don shiga harkokin banza.