Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa, Uncategorized

Sarakuna suke wanzar da zama lafiya a cikin al’umma – Galajen Dass

Alhaji Nuhu Muhammad Bashi shi ne Galajen Mai martaba Sarkin Dass da ke Karamar Hukumar Dass a Jihar Bauchi, a zantawa da Aminiya ya fayyace ayyukan da Galaje ke yi:

Me ake nufi da Sarautar Galaje kuma ina asalin sarautar ?

Sarautar Galaje Sarauta ce da Sarki yake nada mutum mai hazaka da zai rika samo kayayyakin ado da na kawa da za a rika amfani da su a fada, kuma asalin wannan sarauta zumunci a tsakanin mutanen Dass da kasar Borno domin kowa ya sani asalin mutanen Dass daga Borno suka taso suka dawo nan, ka ga alakarmu da su ke nan.  Sannan al’adu da sarautu irin nasu mukan yi amfani da su. Ni ne mutum na farko da Mai martaba ya nada wannan sarauta.

Mene ne aikin Galaje a Masarautar Dass?

Shi Galaje aikinsa nemo dukan wani kaya na sarauta da za a yi amfani da su a fada, kamar sutura da kayan kawa har ma da kayan yaki wanda masarauta za ta yi amfani da su.

Kasancewar wannan a karkashin Galaje yake, shi ya sa idan Sarki zai yi tafiya a kan samu mutane karkashin ofishin Galaje tare da Sarki, kuma su ma sukan sayo kayayyakin da za a iya amfani da su.

Me za ka ce kan ci gaban masarautu a wannan zamani?

Alhamdu lillahi ka san an ce ba a raina mafari, su asalin masarautunmu dukansu in ka duba za ka tarar addini da al’ada ya kafa su, amma tushen martabarsu yana ga addinin Musulunci, musamman mu a kasar Bauchi dukan masarautunmu guda shida cikin tarihinsu akwai nasaba da addini da al’ada. Kai koda al’ada ya fara za ka ga addinin Musulunci ne ya shiga cikinsu ya inganta darajar masarautar da tarihinta. Shi kuma addinin ba ya sauyawa duk da sauyawar zamani. Haka tsarin masarauta yake tsarina na addinin Musulunci ne duk shudewar zamani Sarki ne dai zai ba da umarni a dauki azumi, shi zai ba da umarni a yi Sallah shi ke fara yanka dabbar layyansa kafin sauran al’umma su yi koyi. Wannan yana nuna maka tasirin addini cikin masarautu, haka kuma al’adar Hawan Sallah wadda ke nuna irin jaruman da masarauta ke da su da kuma kayayyakin yaki, kuma wannan yana nuna tasirin al’ada cikin masarautu. Dukan wadannan duk da shudewar zamani har yanzu suna burge al’umma don a kullum za a yi dubban jama’a ne ke zuwa suna kallo suna farin ciki da alfahari suna jin dadi. Haka idan ka duba darajar da sarakunanmu ke da ita duk da shudewar zamani har gobe sarakuna su ne ababen girmamawa cikin jama’a da ma gwamnati. Haka kuma sarakuna su ne ke yin sulhu a tsakanin jama’a, kuma su ke gyara aure da ba da umarni da horon a yi ayyukan alheri kuma jama’a su karba. A takaice dai har gobe su ne ginshikan raya addini da gina zama lafya da kwanciyar hankali a tsakanin jama’a.

Duk da irin wannan martaba da suke da shi cikin al’umma, sha’aninsu na fama da tarnaki yau domin rashin samun irin ikon da ya kamata. Na farko ka ga sarakuna ne ba su da wani hurumi na aiki kundin tsarin mulki sabanin  zamanin da suke kula da kotuna da alkalai da gidajen yari da sauransu, yanzu komai za su yi sai sun nemi tallafin gwamnati hatta tafiya sai sun nemi tallafin gwamnati.

Ka ce ba su da hurumi cikin kundin tsarin mulki yaya za a iya yin gyara?

Gaskiya ra’ayina kan wannan irin na magabata ne, wadansu daga cikin magabatanmu suna ganin sarakuna su ne suka fi cancanta a kula da su a ba su hurumi cikin tsarin mulki kuma a ba su ’yancin cin gashin kansu, kudinsu ya rika shiga hannayensu kai-tsaye ba sai komai in za su yi sai sun bi ta hannun gwamnati ba, walau ta karamar hukuma ko ta jiha. Gaskiya a gyara wannan ya fi amma masu martaba kamar sarakuna a ce ba su da hurumi cikin tsarin mulki kai ka san da gyara a nan. Don sarakuna suke da kasa da kuma jama’ar kasar, in ka samu gari duk lungu da sako ba gida da basarake bai san wanda yake cikin gidan ba.

A karshe wace shawara za ka ba al’ummar masarautar?

Ina so su ji tsoron Allah su kula da ibada su kuma ci gaba da zama masu biyayya ga hukuma da masarautu da shugabannin kamar yadda Allah Ya yi umarni, su kasance masu kaunar zama lafiya, don da zama lafiya ne ake samun dukan ci gaban da ake bukata da samun nasara. Ba mutane kadai ba, har hukumomi kada su rika raina masarauta.

Leave a Reply