Kano Ayau Hausa, RAHOTANNI

Sanyi zai karu a arewacin Najeriya – NIMET

Hukumar binciken yanayi a Nijeriya NIMET ta ce akwai yiwuwar sanyin da ake fuskanta a kasar zai karu nan gaba cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Farfesa Sani Abubakar Mashi, Daraktan Hukumar binciken yanayi ta Najeriya, wato NIMET ne ya shaida wa BBC hakan.

Farfesa ya ce sanyin da ake samu a Nijeriya ya karu ne saboda gudun iskar da ke tasowa daga arewa maso gabas mai kunshe da laima ya karu inda a wasu lokuta har takan kai gudun kilomita 100 cikin sa’a d’aya.

Al’umma da dama ne a kasashen Afirka ta Yamma musamman Najeriya ke kokawa saboda karuwar sanyi a bana.

‘Yan Najeriya da dama na fadin irin halin da suke ciki dangane da yanayin sanyin da ake yi a Arewacin Najeriya a bana.

Wasu dai na cewa ba sa iya fita daga gida zuwa wajen sana’o’insu na yau da kullum, inda wasu kuma ke cewa ba ma sa iya yin wanka.

Sanyin na wannan shekarar ya zo da bazata kasancewar har wuraren da a baya ba su san sanyin ba sosai yanzu sun sani.

A baya dai ba kasafai birnin Abuja na Najeriya ke fuskantar irin wannan sanyi ba, amma a bana al’amarin ba haka yake ba.

Leave a Reply