Kano Ayau Hausa, Siyasa

Sanata Shekarau ya yi watsi da batun ficewa daga NNPP zuwa PDP

Majalisar ƙoli dake da alhakin yanke hukunci kan tsarin siyasar Sanata Ibrahim Shekarau, ta yi watsi da labarin yunkurin Sanatan na ficewa daga NNPP zuwa jam’iyyar PDP.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, a wani taro da majalisar shuran tayi a gidan Malam Shekarau, dake Mundubawa, a Kano, wanda ya dauki tsawon sa’o’i biyar ana la’akari da batun ficewar Sanatan daga NNPP, inda suka yi fatali da wannan magana.

Duk da cewa jam’iyyar NNPP ta bakin dan takarar shugaban kasar ta Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yi zargin cewa bai cika yarjejeniyar da suka kulla da Malam Ibrahim Shekarau ba kafin ya koma jam’iyyar.

“Ka san da kyar Malam Shekarau ya dauki matakin siyasa ba tare da tuntubar majalisar Shura ba,” inji majiya daga majalisar.

Idan za a iya tunawa, Wata jarida ta yanar gizo, ta rawaito shirin Sanata Shekarau na sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, ko wane lokaci daga yanzu.

A cewar jaridar, majiya mai tushe da ke da masaniya kan yunkurin Malam Shekarau da kuma ganawar daban da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar; da abokin takararsa Ifeanyi Okowa da; Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyochia Ayu, ya ce tsohon gwamnan ya “yi yarjejeniya” da PDP kuma ana sa ran nan ba da dadewa ba zai bayyana ficewar sa a hukumance.

Jaridar ta tattaro cewa wani kwamiti mai mambobi 21 zai gana a ranar Talata (yau) da karfe 4 na yamma don kammala shirye-shiryen sauya sheka da kuma hanyoyin magance abinda kaje yazo, bayan sanar da kudirin Shekarau din kamar yadda muka ruwaito daga Jaridar Dimokuradiyya.

Wata majiya da ke da masaniya kan taron ta ce a wani bangare na shirin ficewa don komawa ga dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ya shirya zuwa gidan Malam Shekarau dake a Mundubawa domin ya tarbe shi kafin a fitar da sanarwar.

Sai dai da yake tabbatar da tattaunawar da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, na kusa ga Malam Ibrahim Shekarau ya shaida wa Solacebase cewa babbar jam’iyyar adawa ta tattauna da Malam Shekarau kan ya fice daga jam’iyyar NNPP.

Leave a Reply