Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa

Saboda batan dana abinci ma ya gagare ni ci – Mahaifiyar Janar Alkali

Mahaifiya Janar Muhammad Idris Alkali (mai ritaya) da ya bace a Jos kimanin mako hudu da suka gabata bayan ya baro Abuja zuwa  Bauchi ta ce ba ta iya cin abinci tun lokacin da ta samu labarin.

Bacewar Janar Alkali ta jefa al’ummar kasar nan, musamman na Unguwar Bolawa da ke garin Potiskum a cikin rudani. Hakan ya sa duk inda ka tarar da majalisar matasa ko dattawa maganar da ake yi ke nan.

Janar Alkali, wanda kafin ya yi ritaya shi ne shugaban sashin gudanarwa na Rundunar Sojin Najeriya da ke Abuja, kuma ya fito daga gidan sarautar Alkalin Fika, da ya yi fice a fannin ilimin boko da na Musulunci.

Aminiya ya samu ganawa da mahaifiyar Janar Alkali mai shekara 93 da kuma wadansu daga cikin ’yan uwansa.

A tattaunawa mahaifiyarsa, Hajiya Halima U. Alkali ta bayyana rudanin da ta shiga sakamakon batan da danta ya yi, inda ta ce hatta abinci ya gagare ta ci kuma kafafunta na neman su faskare ta takawa.

Game da ko ta gamsu da kokarin da sojoji suke yi na ganin an gano danta, sai ta ce: “To ai dansu ne, ya bauta wa kasar nan na shekara 35. Saboda haka rashin biyayya ce ga kasa a ce mata ga yadda za ta gudanar da aikinta. Amma dai ina son a kara zage damtse domin ina matukar son in sanya shi a idona.

“Na rasa ’ya’yana biyu kafin shi amma ban taba shiga cikin mawuyacin hali irin wannan ba. Dalili kuwa shi har yanzu ban san halin da yake ciki ba, amma sauran na ga gawarsu kafin a sallace su, a binne su. Shi kuwa ya alla yana hannun masu garkuwa da mutane ko yana ina ne? Ni dai ina rokon a kara zurfafa bincika domin gano mini inda yake don in samu natsuwa,” inji ta

Mahaifiyar ta ci gaba da cewa shi ne danta na takwas kuma a ranar da ya bata ta kira shi da safe domin ta ji muryarsa, ba ta same shi ba da kuma ta kira matarsa domin ta hada su su yi magana sai ta ce mata yana kan hanyarsa ta zuwa Bauchi, amma za ta sanar da shi ya kira ta idan ya isa lafiya. Kwatsam sai aka ce da ita ya bata, abu kamar wasa.

“Daya daga cikin dalilan da suka sa na kira shi, shi ne, domin in jajanta masa abin da ya faru da yaransu (sojoji) a Borno, in kuma yi masa fada cewa su daina tura yara sababbin dauka fagen daga, ana kashe su. Ashe shi ma ya hadu da tasa jarrabawar,” inji ta.

Ta ce “Na mika komai ga Allah saboda kan haka gidanmu ya kafu. Duk kaddarar da ta same mu komai zafinta ba mu kuka. Sai dai mu roki Allah Ya yaye mana.”

Da Aminiya ta tambaye ta a kan rayuwarsa ta kuruciya, sai ta ce, Janar Alkali ya tashi a yaro mai hakali da hazaka da gaskiya da rikon amana da jajircewa. Kuma tun yana karami ba ya son zalunci da cuta.

Ta ce saboda jaruntakarsa, a lokacin akwai wani maganin zazzabi mai daci da yara suke gudu, shi tauna shi yake yi. Haka kuma idan ya fita wasa wajen abokansa kullum sai sun buge shi, amma haka ba ya hana shi fita gobe.

Ta ce ganin karshe da ta yi masa shi ne lokacin da suka je bude aikin ruwa da rundunar soji ta yi a garin Fika, daga baya kuma ya dawo daurin auren ’yar abokinsa.

“A nan ya zauna kusa da ni, muka gaisa, na dauko wata takarda ta mutanen da yake son ya taimaka musu. Ya duba takardar kafin ya tafi. Wannan shi ne karshen ganin da na yi masa,” inji shi

Haka ta kara da cewa yana matukar kula da ita. Ta ce a kullum sai ya ce ba ta da kudi bari ya turu mata saboda ya san mutane na matsa mata.

“Haka kuma ya matsa ya sanya mini kayan daki amma na ce masa ba ni da bukatarsu. Saboda abin duniya bai dame mu ba. Babana alkali ne kuma malami ne, amma saboda zuhudu, shari’a ma a kan tabarma yake gudanar da ita ba.  Haka kuma a bisa tabarma yake kwana har ya bar duniya.

“Saboda haka bisa wannan tarbiyyar na ginu kuma ba zan bar ta ba. Aljanna nake nema saboda duniya ba wajen zama ba ce,” inji ta Ta ce, ta gode wa Allah bisa tarbiyyar ’ya’yanta saboda ba su taba dauko mata magana ba, haka kuma ba su satar kudaden gwamanti.

A hirar da Aminiya ta yi da dan kanensa da ke zaune a gidan, Umar Alkali, ya ce a duk lokacin da Janar Alkali ya zo garin Potiskum, a dakin mahaifiyarsa yake kwana.

“Ba ya da gida mallakin kansa a garin Potiskum, wannan ya sa sun kara shakuwa da mahaifiyarsa. Wanda sakamakon haka ne mutane ke cewa zai yi wahala a ce ba ta samu matsala ba. Amma dai har yanzu lafiyarta lau saboda karfin imanin da Allah Ya ba ta.” inji shi.

 

Leave a Reply