Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa

Rundunar sojoji zata tabbatar da tsaron manoma a Borno

Rundunar sojojin Najeriya ta ce zata tabbatar da yunkurinta akan samarwa manoman jihar Borno tsaro, don samun wadataccen abinci a kasa baki daya.

Daraktan hulda jama’a na rundunar sojojin Najeriya Birgediya Janar  Texas Chukwu, ne ya bayyana hakan yau Alhamis a Maiduguri, a lokacin da mukaddashshin kwamandan dakaru na 7 (GOC) Birgediya Janar Bulama Biu, yake jawabi yayin da kungiyar manoma shinkafa ta Najeriya (RIFAN) suka ziyarci sansanin sojojin a Maiduguri.

Biu ya bayyana cewa, manoman shinkafar suna da gagarumar gudunmawar da zasu bayar wajen samar da wadataccen abinci a kasar. Ya kuma bukaci manoman da su zama masu kiyaye doka wajen harkokin kasuwancinsu.

A lokacin da Shugaban kungiyar RIFAN Alhaji Bulama Mohammed yake jawabi ya godewa rundunar sojojin Najeriya akan kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankunan Arewa maso Gabas.

Leave a Reply