HANTSI, Kano Ayau Hausa

Rufe makarantun Nijar: ‘Rahoton BBC karya ne’

Daga Mani Kasumawa Kalgeri

Na ji an ce BBC sun ce an kulle makarantu a Nijar saboda matsalolin tsaro.
Wannan labarin ba shi da tushe, ƙarya ce tsagwaronta daga bakinsu….
Tsarin karatun Nijar, tsari ne da aka tsara yake bin yanayin mutanen cikinta waɗanda akasarinsu manoma ne da makiyaya.
Asalin Nijar ƴan kasuwa ma ba su yawaita ba. Balle ma’aikatan gwanati. A ƴan baya-bayan nan ne ma aka samu cigaba, kasuwa ta yawaita, ƴan boko suka ɗan kai adadin da ake da.
Lura da haka ne ya sa hutun karatun boko ake ba da shi sau ukku:
Na farko kwanaki goma.
Na biyu ma haka.
Na ukkun ake jinkirtawa sai faɗuwar damina a saki makarantu har sai an yi watanni ukku zuwa huɗu saboda idan ba haka ba, mutanen da suka fi yawa a ƙasar, wato manoma, ba za su bar ƴaƴansu su je makaranta ba. Ta yaya mutumin karkara wanda da noma ya dogara, ya tara yaransa biyar ya kai su makaranta shi ya tafi gona?!

Don haka tun fil’azal haka makarantun bokonmu suke, daga watan June zuwa farkon Satumba hutu ne babba wanda a cikinsa aka ba malaman makaranta da ɗalibai bonus don su tafi su yi noma.

Mani Kasumawa Kalgeri ne ya wallafa wannan bayanin a shafinsa na Facebook

Leave a Reply