Dan wasan Portugal, Cristiano Ronaldo zai zo kungiyar Newcastle idan kungiyar ta samu shiga Gasar Zakarun Turai ta badi.
Haka na kunshe ne a cikin yarjejeniyar da dan wasan ya sa hannu da Kungiyar Al Nassr ta Saudiyya, wadda take da alaka da kungiyar ta Newcastle ta Ingila.
Ronaldo dai ya sauka a Birnin Riyadh domin fara wasa da sabuwar kungiyarsa, inda zai kasance dan kwallo mafi daraja a duniya.
A wani bangaren kuma, akwai alama Ronaldo din zai sake haduwa da Sergio Ramos da Luka Modric a kungiyar ta Newcastle a gasar ta badi, domin kungiyar ta fara zawarcin ’yan wasan guda biyu.