Rikicin shugabanci ya kaure tsakanin wasu `yan jam`iyyar PRP da ke ikirarin cewa su ne `ya`yanta na asali, da kuma wasu da suke yi wa kallon baki a jihar Kano da ke Najeriya.
Mutanen da aka taras a jam’iyyar sun yi zargin wasu na yunkurin kwace shugabancinta daga hannunsu.
Sai dai bangaren da ake yi wa kallon sabbin-shiga ne a jam`iyyar PRPn sun yi zargin cewa abokan hamayyar cikin gida ne ke zuga masu jayayya don cimma wata manufa ta siyasa.
“Sun yi hakan ne don ganin jam`iyyar na samun tagomashi,” in ji su kamar yadda BBC ta ruwaito.
Masu ikirarin cewa su ne `yan asalin jam’iyyar sun ce sabbin shiga jam`iyyar sun saba wa akidar PRP da manufofinta na jibantar talakawa, sun juya tsarin jari-hujja, don haka ba za su saurara musu ba.
Mallam Mukhtar Tanko Zango wanda ke ikirarin cewa shi ne shugaban jam`iyyar PRP na jihar Kano, ya ce shigar wasu jam`iyyar ta sa an yi watsi da shugabancinta, an kuma dora jam`iyyar a kan tafarkin da ya yi hannun-riga da wanda magabata suka assasa ta a kai.
`Yan jam`iyyar PRPn, wadanda ke ikirarin cewa `yan na-gada ne tun iyaye da kakanni sun yi zargin cewa jam`iyyar na fama da mamayar wasu da suka bayyana da `yan boko, wadanda suka yi mata shigar rana-tsaka suna kokarin wargaza ta.
Jam`iyyar PRP da ta kwashe lokaci mai tsawo tana zaune lafiya da `ya`yanta a Kano, ba a fara jin kansu ba sai bayan zabukan fid da gwanin da aka yi a jihar, inda wasu manyan `yan siyasa suka yi kaura daga jam`iyyunsu na asali zuwa jam`iyyar PRP bayan sun nemi takara ba su samu yadda suke so ba.
Jam`iyyar PRP da takwararta ta PDP dai su ne manyan jam`iyyun hamayya a jihar Kano.
Kuma yayin da PDP ta jima tana fama da nata rikicin shugabanci, kasancewar wata maganar ma na kotu, PRP za a iya cewa watakila wutar da ke neman cinye ta ba ta wuce a taru a kashe ta ba duk da cewa ita ma jam`iyyar APC mai mulki na da irin nata matsaloli ko larurar.
Masana kimiyyar siyasa dai na cewa idan jam`iyyun hamayyar ba su gaggauta dai-dai ta gidajennsu ba, to, watakila APC za ta samu damar rawar-gaban-hantsi a babban zaben da ke tafe.