Kungiyar Iyayen Yara da Malamai ta Kasa (PTA) reshin Jihar Nasarawa ta koka cewa rayuwar daliban makarantun firamaren gwamnatin jihar tana cikin hadari dangane da yadda gine-ginen makarantun suka soma nuna alamun rushewa bayan shekara uku da kammala gina su.
A lokacin da wakilinmu ke zagaye don gudanar da bincike a kan lamarin ya gana da Shugaban Kungiyar Iyayen Yara ta Jihar, Mista Umaru Ebenya, inda ya ce makarantun da aka gina kimanin shekara 3 da suka gabata sun soma nuna alamun rushewa. Ya ce gwamnati ba ta bukaci taimako ko gudunmawar kungiyar ba a matsayinsu na masu ruwa-da-tsaki a lokacin da ake gina makarantun balle su sa ido domin tabbatar an yi shi cikin tsari saboda a dade ana cin moriyarsu.
Ya ce “Rahotannin da nake ci gaba da samu daga fadin jihar nan, sun tabbatar da cewa wadannan makarantun firamare na gwamnatin jihar da ake kira Ta’aal Modern Primary Schools da aka gina kwanan nan a sassan jihar, sun fara nuna alamun rushewa sakamakon aiki mara tsari da inganci da wadanda aka ba su kwangilar aikin suka yi.”
Ya bukaci gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa don kaurace wa rushewar da sauran illolin da ka iya biyo bayansa, musamman a yanzu da yaran suka fara komawa makarantu don ci gaba da daukar darasi.
Wadansu iyayen dalibai da wakilinmu ya zanta da su game da lamarin da suka bukaci a sakaya sunayensu, sun nuna fargaba da takaicinsu; suna cewa idan makarantun na Ta’aal Primary din da aka gina, cikin shekara uka kacal za su fuskanci irin wannan lamari, me zai faru da wasu ayyukan ci gaba da gwamnati ta yi a jihar nan da shekara 8 masu zuwa?
Wani mai suna Akulo James mazaunin garin Nasarawa-Eggon a jihar, ya alakanta barazanar rushewar ga mummunan ayyuka marasa tsari da aka yi. Ya ce “Kamar yadda ka sani, wadannan sababbin makarantun firamare na gwamnati suna cikin manyan ayyukan Gwamnatin Umaru Tanko Al-Makura amma na kasa gane yadda ake sake yi musu kwaskwarima, ana canja tsarinsu da sauransu tun ba a dade da fara amfani da su ba. Kuma na lura cewa ba gine-ginen makarantun ne kawai ke barazanar rushewa ba, har da wasu manyan hanyoyi da gwamnatinsa ta gina musamman a nan yankinmu na Nasarawa-Eggon, bayan shekara 2 kacal da aka gina su.”
A wani labarin Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a jihar ya bai wa wadansu ’yan kwangila aikin yi wa makarantun kwaskwarima; musamman na yin sababbin filoli ga gine-ginen cikin gaggawa don kaurace wa rushewar. Wadannan makarantun firamare na gwamnatin jihar na zamani da aka gina a kananan hukumomin jihar 13, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo ne ya kaddamar da wasu daga cikinsu.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a kan lamarin, ya gano cewa bayan wadannan sababbin makarantun firamare na Ta’aal, wasu kananan makarantun yara na gwamnati a jihar ma sun lalace. Wadannan makarantu sun hada da wadda ke kusa da babban hanyar Lafiya zuwa Jos a cikin garin Lafiya da wadanda ke garuruwan Nasarawa-Eggon da Akwanga da Shabu da Kwandare da Wamba da sauransu, da suke bukatar kwaskwarima, ko sake gina su.