BABBAN BANGO

Obasanjo yana bukatar likita ya duba masa lafiya- Buhari

A martanin da gwamnati ta mayar kan wasikar ta Cif Olusegun Obasanjo, Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, ya bayyana wasikar a matsayin wani yunkuri na wadansu ’yan siyasar da suka gaza ja da Shugaba Buhari a siyasance suka koma cin dunduniyarsa.

Gwamnatin ta ce ga alama Cif Obasanjo yana bukatar kwararren likita ya duba lafiyarsa, inda ta yi masa fatan samun lafiya cikin gaggawa. “Shawara a gare shi, shi ne ya nemi likita, ya nemi magani. Muna yi masa fatan Allah Ya ba shi lafiya,” inji sanarwar.

Gwamnatin ta kuma bayyana Obasanjo da mutum mai hassada saboda ya san Shugaba Buhari ya fi shi martaba a idon duniya. Ta ce Cif Obasanjo yana juya wa duk mutumin da ya ga ba zai kyale shi ya yi abin da ya so ba, kuma ya fitar da wasikarsa tasa ce domin ya rasa mafita ta ci gaba da tatsar haramtacciyar dukiyar da ya saba yi a shekarun baya.

Kakakin Shugaban Kasar ya ce zaben Shugaban Kasa da za a yi a watan gobe zai kasance sahihi kamar yadda Shugaba Buhari ya yi alkarwari ga kasar nan da duniya baki daya.

Kakakin Shugaban ya ce, “Abin da muke so mu nuna musu shi ne, kayen da suka sha a wancan karon somin tabi ne, kuma wanda za su gani a zabe mai zuwa sai ya rugurguza su a siyasance. Daga wannan lokacin ba za a sake jin kansu ba, domin karshen siyasarsu ya zo. Jama’a za su kada kuri’a kuma za su yi musu kayen da ba su taba tsammanin zai same su ba.”

Sanarwar ta bayyana Cif Obasanjo da babban matsoraci, inda ta zarge shi da karkatar da Dala biliyan 16, kudin da ta ce an ware domin samar da wutar lantarki a lokacin mulkinsa, aikin da ta ce ba a yi ba, don haka ta ce yana cike da tsoron ranar da za a tuhume shi ya bayyana abin da ya yi da kudaden.

A kan batun yaki da kungiyar Boko Haram kuwa, Malam Garba Shehu ya yi watsi da ikirarin Cif Obasanjo cewa gwamnatin Buhari na da hannu wajen fadawar da Libya ta yi cikin rikici. Garba Shehu ya ce “Ka dubi Najeriya, ka ce wai Boko Haram a karkashin mulkin Shugaba Buhari ta fi karfi, wannan magana ce ta mafarki.Ko kuma ka zargi Shugaba Buhari don kasar Libya ta rushe… ai a lokacin gwamnatinsu ta PDP ce ke mulki, wane mataki suka dauka a kai?”  Sanarwar ta yi watsi da wasikar ta Cif Oasanjo musamman inda ya ce Shugaba Buhari ya shirya murde zaben Shugaban Kasa da zai gudana kasa da mako hudu masu zuwa.

Garba Shehu ya ce abin takaici ne a ce dan shekara 90 da haihuwa ya zama “tsohon makaryaci,” kuma Shugaba Buhari zai ba marada kunya.

Leave a Reply