GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Ni ban Musulunta ba-Drogba

Tsohon dan wasan kwallon kafar Ivory Coast Didier Drogba ya musanta labarin da ke cewa ya musulunta, bayan da wani malami ya wallafa hotonsa tare da tsohon dan kwallon suna addu’a a shafinsa na Tuwita.
Malamin ya wallafa hoton, tare da cewa tsohon dan kwallon ya musulunta.
To sai dai a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Drogba ya ce ba musulunta ya yi ba, addu’a kawai yake yi wa musulman kauyensu bayan da ya ziyarci kauyen nasu.
Ya bayyana cewa lokaci ne na nuna ”’yan uwantaka,” kamar yadda BBC ta ruwaito.
Daga baya malamin mai suna Mohamed Salah ya goge sakon da ya wallafa din, inda ya ce Drogba ba musulunta ya yi ba, to amma kuma zai ci gaba da yi masa addu’ar musulunta.

Leave a Reply