BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ni Atiku zan zaba a zaben 2019-Sheikh Sambo Rigachikun

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya kuma jigo a kungiyar Izala, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, ya ce dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar zai zaba a zaben 2019.

A karshen makon jiya ne kungiyar Izala a kasar, ta bukaci mabiyanta da su zabi Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, wanda yake neman wa’adi na biyu.

A tattaunawar da wakilinmu Mustapha Kaita ya yi da Shiekh Sambo, ya bayyana dalilan da ya sa yake goyon bayan Atiku Abubakar.

“Zan zabi mutumin da ya fi taimakon addinin Musulunci da taimakon jama’a da kuma amfanar da mutanen kasa,” in ji shi.

Malamin dai ya bayyana karara cewa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne zabinsa a 2019 kamar yadda BBC ta ruwaito.

Har ila yau, malamin ya yi ikirarin cewa ya kwashe shekara 30 yana tare da Atiku, inda ya ce dan takarar ya “gina masallatan Juma’a fiye da 100.”

Ana dai ci gaba da samun rabuwar kai a bangaren malaman Izala a Najeriya.

A ranar Asabar ne Kungiyar Izala daya daga cikin manyan kungiyoyin addinin Islama a Najeriya ta ce Shugaba Buhari take goyon baya a zaben 2019.

Shugaban kungiyar na kasa Shiekh Abdullahi Bala Lau ya ce sun yanke shawarar ne bayan wani taro na kasa da suka gudanar.

Ya ce sun lura yadda ake fuskantar lokacin zabe mawuyaci, “ya kamata a yi saitin al’ummar Musulmi kan abin da ya kamata.”

“Allah ya kawo saukin rigingimu da tashin bama-bamai dalilin zuwan Shugaba Buhari, illa dan abin da ya rage na fitintinun, Allah zai kawo saukinsu,” in ji Sheikh Bala Lau.

Leave a Reply