Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta gargadi ‘yan kasar da su ƙaurace wa amfani da kayan kwalliyar da kan sauya fatar jikin bil adama daga baƙa zuwa fara.
Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Olusayo Akintola ya aike wa manema labarai ranar Lahadi kamar yadda muka kalato daga BBC.
NAFDAC ta umarci a kama da gurfanar da wadanda suke tallata wannan sinadari ba tare da sahalewar hukumomin kasar ba.
Ta ce an haramta wadannan kayayyaki, saboda suna da lahani ga fata da wasu sassan bil adama kamar hanta da koda.