Fadar shugaban Najeriya ta nuna goyon bayanta ga kalaman gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa’i kan barazanar da ya yi ga tsoma bakin ‘yan kasashen waje ga sha’anin zaben kasar.
Gwamnan El-Rufai ya ce duk wani dan kasar wajen da ya tsoma baki a zaben Najeriya na 2019 za a koma da gawarsa.
Ya fadi haka ne a shirin Tuesday Live da ake gudanarwa ranar Talata a gidan talabijin na kasa NTA.
Mai taimakawa shugaban Najeriya kan watsa labarai Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa sun gamsu da bayanan na gwamnan Kaduna.
“Mummunar fahimta aka yi wa kalaman da gwamnan ya yi.”
“Ba ya da nufin ya nemi a raunata wani ko halaka wani, ko dan Najeriya ko dan kasar waje dangane da harakar zabe.”
“Magana ce ta kare kishin kasa da mutuncin kasarsa ta Najeriya,” in ji shi.
Kalaman gwamnan na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce. inda wasu suke ganin bai dace ace gwamna kamarsa ba ya fadi haka a daidai wannan lokaci da hankalin duniya ya karkata ga zaben Najeriya.
Wasu sun yi wa kalaman fassarar cewa, gwamnan yana nufin za a farwa ‘yan kasashen waje da suka shigo Najeriya domin sa ido ga zaben kasar.
Amma gwamnan ya kare kalamansa inda kakakinsa Samuel Aruwan ya shaida wa BBC cewa gwamnan na nufin kasashen su mutunta ‘yancin cin ganshin kan Najeriya.
Garba Shehu ya ce a yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya babu inda aka yadda wata kasa ta dauki lamurran cikin gida na wata kasa ta tsoma baki ko ta yi karanbani ko kankanba akai ba.
A sanarwar da ya fara tura BBC, Garba Shehu ya ce “Mun ji kalaman da gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya yi kan kiran da ‘yan adawa ke yi ga kasashen waje su tsoma baki ga harakokin cikin gidanmu, za mu ce ya kamata kalamansa su kawo karshen zancen. Ba wani abu ba ne da za a tada kura akai,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce gwamnan ya yi kalaman ne da nufin kare manufofin kasa, kuma hakan ya nuna El Rufa’i da jam’iyyar APC da sauran ‘yan takara sun yi imani da mulkin demokuradiya ta hanyar zabe.
Kuma ba za su yarda da duk wani rikici ba kan ‘yan kasa da kuma baki daga kasashen waje.
Ta kara da cewa, gwamnatin Tarayya karkashin shugaba Muhammadu Buhari za ta yi aiki tare da masu sa ido kuma ba za a taba juya masu baya ba a harakokin zaben kasar.
Sanarwar ta kuma ce, fadar shugaban kasa na tabbatar wa ‘yan Najeriya da sauran al’ummar duniya cewa shugaban kasa zai yi duk abin da ya dace iya ikonsa domin tabbatar da ganin an yi karbabben zabe a fadin kasar.
“‘Yan adawa ne ke neman hanyoyin da za su muzanta jam’iyyar APC da gwamnatin Buhari.”
“Gaskiya ce El Rufa’i ya fito ya fada cewar babu tababar zabe za a yi na gaskiya na hakika.”
“Duk kuri’a sai an kirga, kuma mai ita sai an ba shi kayansa,” in ji shi kamar yadda BBC ta kalato.
Ya kuma ce an ba hukumar zabe cikakken hakkinta, abin da ba’a taba yi ba a tarihin Najeriya, domin ko naira daya ba su bin gwamnati daga kudaden da suka nema naira biliyan 180