Manoma a karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna sun ce, yawan garkuwan da ake yi da jama’a ya tilasta masu barin gonakinsu.
Wasu daga cikin manoman sun bayyana cewa, a yanzu haka ba su da damar girbe abin da suka shuka a gonakinsu.
Wadanda manoman ke zargi da yin garkuwan da mutane su ne, Fulani dauke da muggan makamai dake yankin kusan kilomita uku zuwa tashar jirgin kasa na Rigasa. Wani manomi Malam Sabo ya ce, a duk lokacin da suka je gonakinsu sai an yi garkuwa da wani don neman kudin fansa.
Kauyukan da aka fi yin garkuwan sun hada da: Gurguzu da Kwate da Maguzawa Mai Giginya da Kwaten dan Masani da kuma Faka.