BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Mubarak Bala ya amsa laifin aikata sabo a gaban kotu

Wata babbar kotu a Kano ta sake aikewa da Mubakar Bala zuwa gidan gyaran hali, saboda ci gaba da tsare rayuwarsa da kuma gazawar lauyoyinsa na gabatar wa kotun da cikakaken takardun da za su tabbatar mata cewar yana fama da rashin lafiya.
An karanto ma Mubarak Bala caji 14 da ake tuhumarsa a kai na yin sabo.
Yayin zaman kotun, an karanto masa sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook, wadanda yayi kalaman batanci ga addinin Musulunci.
Ya amsa dukkan caji 14 da aka karanto masa da cewar ya aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.
Ganin haka sai lauyansa ya roki kotun ta ba shi damar ganawa da wanda yake wakiltar, wato Mubarak Bala, kuma bayan ta amince, ya yi kokarin nuna ma sa tasirin cewa ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa.
Amma bayan da lauyan ya sanar da kotun cewa Mubarak Bala na son sauya amsar da ya bayar a gaban kotun, sai alkalin ya sake tambayar wanda ake tuhumar ko haka lamarin yake.
Mubarak Bala ya sanar da kotun cewa ba zai sauya amsa laifinsa da ya yi a gaban kotun ba.
Alkali kotun ya tambaye shi ko ya fahimci nauyin abubuwan da yake cewa, kuma wanda ake tuhumar ya amsa cewa ya fahimci komai.
Ya kara da cewa babu wanda ya tursasa masa don ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa. Sannan ya ce babu wanda yayi masa wani alkawari, ko ya sanya masa wani ra’ayi, sai dai ya bukaci kotun ta yi masa sassauci da kuma adalci.
Wakilin BBC da ke kotun ya ce kotun na ci gaba da sauraron shari’ar.
Tushe: BBC Hausa

Leave a Reply